Skip to content
الإسرَاء /

Aya 78

17 : 78
الإسرَاء Ayoyi 111
17 : 78

أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمۡسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيۡلِ وَقُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِۖ إِنَّ قُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِ كَانَ مَشۡهُودٗا

Ka tsayar da salla a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.

Explanation & meanings · 2
  1. Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana.
  2. Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar Alfijir.