الفضل بن العباس
الإسم
Fadalu dan Abbas
اسم الشهرة
Alfadhl Bin Al-Abbas -Allah yarda da su-
نبذة مختصرة
Fadalu dan Abbas dan AbdulMudallabi dan Hashim dan abdumanaf bakuraishe, Abu Muhammad kuma Abu Abdullah, sahabi ne mai daraja, dan baffan Ma’aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh— shi ne babba a duk ‘ya’yan Abbs, Abbas ya kasance ana masa alkunya ne da shi, ya halarci bude Makkah tare da annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh— shekara ta 8, ya yi yaki tare da shi a Hunain, kuma ya kasance cikin wadanda suka tabbata tare Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cikin Alhul Baiti da kuma Sahabbai, a lokacin da mutane suka juya da baya suka gudu, kuma ya halarci Hajjin bankwana tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh— ya dora shi a bayansa akan dabba tun daga Muzdalifa har zuwa Muna, ana cewa da shi: goyon Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Hakika Fadlu (Falalu) ya halarci rasuwar annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma da shi aka yi masa wanka, shi ne wanda ya kasance yana zubawa Sayyidina Aliyu dan Abu Dalib ruwa. Marawaita sun yi sabani ashekarar rasuwarsa, mafi inganci a ciki ita ce ya fita jihadi ne zuwa Sham, sai ya rasu a annobar da aka yi a Tudddan golan, ta bangaran Jodan, shekara ta 18, a halifancin Sayyidina Umar dan Khaddab.