أم كلثوم بنت نبينا محمد بن عبد الله القرشية الهاشمية
الإسم
Ummu Kulsum diyar annabinmu Muhammad dan Abdullah bakuraishiya daga gidan Hashim
اسم الشهرة
Ummu Kulsum Allah ya yarda da ita
نبذة مختصرة
Ummu Kulsum diyar Mustafa annabinmu Muhammad dan Abdullah dan AbdulMudallabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh— bakuraishiya daga gidan Hashimu, babarta ita ce Khadijah diyar Khuwailid, Utbatu dan Abu Lahab ne ya aureta tun kafin annabta, a lokacin da aka aiko Ma’aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi— kuma Allah ya saukar da TABBAT YADAA, sai baban shi Abu Lahab ya ce da shi: Kaina da kanka haraun ne idan ba ka saki ‘yar sa, sai ya rabu da ita, daman ba su tare ba. Ba ta gushe ba tana Makkah tare da babanta-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ta musulunta lokacin da babarta ta musulunta, ta yi wa Ma’aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-caffa tare da ‘yan uwanta mata a lokacin da mata suka yi masa caffa (mubaya’a), ta yi hijira zuwa Madina ba ta gushe ba a Madina, a lokacin da Rukayya diyar Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta rasu sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shii- ya aurar wa Sayyidina Usman dan Affan da ita, hakan kuwa ya kasance ne a watan Rabi’ul Awwal, shekara ta uku bayan hijira, ta tare a wurinsa a watan Jumadah Akhira na shekarar, ba gushe ba awurinsa har ta rasu ba ta haifa masa komai ba, a shekara ta 9, bayan hijira.