الحسن بن علي بن أبي طالب
الإسم
Alhassan dan Aliyu dan Abi Dalib
اسم الشهرة
Alhasan Dan Ali -Allah yarda da su-
نبذة مختصرة
Alhassan dan Aliyu dan Abu Dalib bahashime kuma bakuraishe, Abu Muhammad, jikan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, an haifeshi shekara ta 3 da hijira, shi ne na biyar din halifofi masu shiryarwa, kuma na karshansu. An haifeshi a Madina, Babarsa ita ce Fatima Zahara’u diyar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne babba a ‘ya’yanta, kuma na farkonsa, ya kasance mai hankali, mai hakuri mai son alheri, mai azanci cikin mafiya kyawun muta ne a magana da kwarijini, ya yi Hajji sau ashirin da kafa, Alhassan ya sauka daga halifanci ya mikawa Mu’awiya shugabanci shekara ta 41, aka kira wannan shekarar shekarar hadin kai, saboda haduwar kan Musulmai akan kalma guda, sai Alhassan ya dawo Madina inda ya zauna anan har zuwa rasuwarsa inda aka sa masa guba a wani zancan, halifancinsa watanni shida da kwanaki biyar, ya rasu shekara ta 50 bayan hijira.