الحسن بن يسار البصري
الإسم
Alhassan dan Yasar Albasari
اسم الشهرة
Alhassanul Basari
نبذة مختصرة
Alhassan dan Yasar Albasari, Abu Sa’id, Tabi’i ne malami amintacce yana da yawan Hadisai, an haifeshi a Madina shekara ta 21, ya kasance limamin mutanan Basrah, kuma malamin al’umma a zamaninsa, shi ne daya daga cikin malamai na fikihu masu fasaha, gwaraza masu ibada, ya zauna a Basrah, kuma yana da kwarjini a zukata, ya kasance yana zuwa wurin shugabanni, sai ya umarce kuma ya hanesu, ya kasance akan gaskiya, ba ya tsoron zargin mai zargi, shi da Hajjaj dan Yusuf sun fafata, hakika ya kubuta daga cutarwarsa, lokacin da Umar dan Abdul’Aziz ya zama shugaba sai ya rubuta wa Alhassanul Basari wasika cewa: Ni an jarabce ni da wannan lamarin, bincikamin wadanda za su taimakamin. Sai Alhassan ya rubuta masa: Amma wadannan mutanan duniyar nan ba za su yi maka ba, Amma wadanda lahira ce a gabansu to ba kai ne a gabansu ba, ka nemi taimakon Allah, ya rasu a shekara ta 110, bayan hijira.