Skip to content

حذيفة بن حسل بن جابر العبسي

الإسم

Huzaifa dan Hasal dan Jabir Al’abasi

اسم الشهرة

Huzaifa Dan Yamani -Allah ya yarda da shi-

نبذة مختصرة

Huzaifa dan Yaman Al’abasi, babansa ya kasance ya taba kashe wani, sai ya gudu zuwa Madina, sai ya yi kawance da Banu Abdil Ash’hal, sai mutanansa suke kiransa mutumin Yaman, saboda ya yi kawance da yamanawa, sai ya auri babar Huzaifa, sai kuma aka haifa shi a Madina, Huzaifa shi da babansa sun musulunta, ya halarci yakin Khandak, da wadanda suka zo bayan shi, Umar ya tura shi aiki a Mada’in, bai gushe yana wurin ba har ya rasu, bayan kashe Usman da yi wa Aliyu mubaya’a da kwana arba’in, ya zo a cikin Bukhari da Muslim cewa Abu Darda ya cewa Alkama: A she a cikinku ba akwai Ma’abocin sirri ba ? Wanda babu wanda ya san sirrin sai shi? Yana nufin: Huzaifa. Kuma dai a cikin Bukhari da Muslim Daga Umar cewa ya tambayi Huzaifa dangane da fitina , Huzaifa ya halarci bude Iraki, ya rasu a shekara ta 36 bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
معرفة الصحابة لأبي نعيم (2/ 686) الاستيعاب في معرفة الأصحاب (1/ 334) تاريخ بغداد (1/ 505) أسد الغابة (1/ 468) تهذيب الأسماء واللغات (1/154) الأعلام للزركلي(2/171)