Skip to content

Idan aka ce da kai: shin addu’a Ibada ce?

السؤال

Idan aka ce da kai: shin addu’a Ibada ce?

الجواب

Amsa: Sai ka ce: Addu’a tana daga cikin manyana ibadu, kamar yadda Allah yace: “kuma ubangijinku yace: ku roqe ni zan amsa muku, lallai waxanda suke girman kai da barin bauta ta, to za su shiga jahannama sun a qasqantattu (Gafir 60) a cikin hadisi manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace addu’a itace ibada (tirmidhi ne ya ruwaitoshi. Kuma saboda muhimmancinta da girmanta a addini akwai ayoyi fiye da xari uku da suka zo a alqur’ani akanta. Ita addu’a nau’I biyu ce: addu’a ta ibada da addu’a ta roqo, kuma kowacce daga ciki tana Damfare da ‘yar uwarta

Addu’ar Ibada itace: bin Hanya izuwa ga Allah mai girma don neman afkuwar wani abin da ake nema ko ije wani abin baqin ciki ko yaye cuta ta hanyar tsarkake ibada gare shi, shi kaxai. Allah mai girma yace: da kuma zun nun lokaci da ya tafi yana mai fushi, har ya yi zaton ba za mu yi ikon mu akansa ba, sai ya yi kira a cikin duffai ya ce babu abin bauta sai kai, tsarki ya tabbata a gareka, lallai ni ina cikin azzalumai, sai muka amsa masa, muka tserar da shi daga baqin ciki, kuma kamar haka muke tseratar da muminai. (Anbiya 87 -88)

Addu’ar roqo: ita ce roqon abin da zai amfani mai roqon na daga jawo wani amfani ko yaye wata cuta. Allah mai girma yace: ya ubangijinmu lallai mu mun yi imani, ka gafarta mana zunubanmu kuma ka kiyaye mu Azabar wuta (Ali Imran 16).

Addu’a da kowanne irin nau’I aka yi ta, ita ce tsantsar ibada, kuma tafi kowacce ibada ibada sauqin yi, da kuma girma matsayi ta amfani, ita ce hanya mafi qarfi wajen tare abin qi da samun abin nema da yardarm Allah.