Mafi Yawan Bincike
Tace sakamako
Katuna 116
الموضوعات
التصنيف الشرعي
Amsa / sai ka ce: Babu wanda ya san gaibi sai Allah babu kuma mai rayar da matattu sai Allah , dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : Kuma da na kasance ina sanin gaibi, da lallai ne na yawaita daga alheri, kuma cuta baza ta shafeni ba . (al-a`araf : 188) . Yayin da manzon Allah mai tsira da aminci ya kasance shi ne mafificin halitta bai san gaibi ba to wanda yake koma bayan sa shi ne mafi cancanta kuma mafi dacewa da ace bai san gaibi ba
Kuma limaman nan guda hudu (Abu Hanifa, Imamu Malik, Imamu shafi`I, da Imamu Ahmad) sun hadu bisa cewar duk wanda ya kudurce a zuciyar sa cewa manzon Allah mai tsira da aminci yana sanin gaibi ko yana rayar da matattu, to shi mai ridda ne daga musulunci, saboda ya karyata Allan nan da ya umurci manzon sa mai tsira da aminci da ya fadawa mutane da aljanu : Ka ce: ba zan ce muku a wurina taskokin Allah suke ba, kuma ba na sanin gaibi, kuma ba na gaya muku cewa ni mala`ika ne, ba na bin komai sai abinda ake yin wahayi zuwa gareni. (al-an`am: 50). Allah madaukakin sarki kuma ya ce: Lallai Allah a wurinsa kawai sanin sa`a yake (tashin alkiyama), kuma shi yake saukar da ruwan sama, kuma shi ya san abinda ke cikin mahaifannai, kuma babu wata rai da ta ke sanin me zata aikata gobe, kuma babu wata rai da ta ke sanin a wace kasa zata mutu, Lallai Allah masani ne mai kididdigewa (lukman: 34). To manzon Allah mai tsira da aminci baya sanin komai daga gaibi sai kawai abinda Allah yayi wahayi da shi zuwa gareshi, kuma ya sanar da shi shi kadai, kuma manzon Allah mai tsira da aminci babu wata rana da yayi da`awar cewa shi ya rayar da daya daga cikin sahabban sa ko daya daga cikin `ya`yansa wadanda suka rasu kamin shi. To kuma ta yaya wadanda suke komabayan annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi
Amsa: Sai ka ce: Duk wanda ya kasance mumini mai tsoron Allah to shi waliyyi ne a wurin Allah, dalilin haka fadin sa Allah madaukaki: To, lallai ne masoyan Allah babu tsoro a kansu, kuma baza su kasance suna yin bakin ciki ba, Wadanda suka yi imani kuma suka kasance suna yin takawa. (Yunus: 62-63). Ba kebantacciya ba ce ga wani daga cikin muminai banda wani, saidai matakan ta suna tserewa juna (wani yana iya fin wani), kuma takawa tana nufin: aikata abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi umurni da kuma nisantar abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi hani ga barinsa, kuma kowane mumini yana da walittaka gwargwadon imanin sa da Biyayyarsa.
Amsa/ Sai ka ce: Duk wanda ya kasance waliyyi ba daga cikin annabawa ba to shi ba kubutacce ba ne daga afkawa cikin kanana da manyan laifuka, hakika hakan ya faru ba sau daya ko sau biyu ba daga manyan waliyyai da salihan bayi wasu daga cikin zame-zame da tuntube da zurme-zurme, saidai cewa su suna gaggauta tuba da komawa ga Allah, sai Allah ya gafarta musu
Amsa: To sai ka ce: Ingantaccen zance shi ne cewa shi khidr annabi ne daga Annabawan Allah, ya rasu gabanin Haihuwar Annabi mai tsira da aminci- saboda Allah madaukaki ya ce: Kuma bamu sanya dauwama ga wani mutum ba a gabanin ka, shin to, idan ka mutu to, su ne madauwama?. (Al-anbiya: 34). Kuma da ace ya kasance a raye da ya bi manzon Allah mai tsira da aminci- kuma yayi yaki tare da shi, saboda annabin mu mai tsira da aminci an aiko shi zuwa mutane da aljanu baki daya, Allah madaukaki yace : kace ya ku mutane lallai ni jakadan Allah ne zuwa gareku baki daya. (Al-a`araf: 158) Kuma Annabi mai tsira da aminci ya ce: (Yanzu baku ga wannan daren naku ba, hakika a duk karshen shekara dari daga gareta, babu daya daga cikin wanda ke a ban kasa da zai wanzu). Bukhari ne ya rawaito. Kuma wannan shi ne dalilin da ke nuni bisa cewa khidr matacce ne daga cikin Matattu, akan haka ne to shi baya jin kiran wanda duk ya kirashi, kuma baya shiriyar wanda ya bace ga barin hanya ta kwarai a yayin da ya nemi da ya shiryar da shi. Kuma abinda ake ambatawa ga wasu mutane na labirin haduwa da shi da kissoshin ganin sa da zama da shi da daukar ilimi daga gare shi, wannan duk rudu ne da karyace-karyace a fili wanda basa rudar da wanda Allah ya Azurta shi da ilimi da lafiyayyen hankali da Basira
Amsa: Sai kace: Matattu basa ji saboda fadin Allah Madaukaki: Kuma kai baka kasance mai jiyarwa ba ne ga wadanda ke cikin kaburbura. (Fadir:22). Da kuma fadin sa: Lallai kai (ya Muhammad) baka jiyar da matattu. (an-namli:50) Kuma basu iya bada amsa ga wanda ya kira su, Allah madaukaki ya ce: Kuma wadanda kuke kira wanda ba shi ba, ba su mallakar ko bawon kwallon dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun ji ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafircewa shirkarku, kuma babu mai baka labari kamar wanda ya sani (faadir:13-14) Da kuma fadin Allah madaukaki: Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran) Shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5)
Amsa: Sai ka ce: Su wadan nan Muryoyin Shaidanun Aljanu ne, suna Rudar Jahilai da cewa wannan sautin ma`abicin kabarin ne ta yadda har sai sun fitinance su sun cakuda musu addinin su sun batar da su, alhali su ma`abota kabarin basa ji kuma basa amsawa ga wanda yake rokon su ko mai kiran su da nassin kur`ani mai girma, Allah madaukaki ya ce: Hakika lallai ne kai baka jiyar da matattu.(An-namli: 80). Allah madaukaki ya kuma cewa: Idan kun kira su basa jin kiran naku. (Fadir: 14) Allah madaukaki ya kuma fada: Kuma kai ba mai jiyar da wadanda ke cikin kabur-bura ba ne.(Fadir: 22) To ta yaya za su amsa musu alhali su suna wata duniyar ta barzahu, basu da wata alaka da ahalin wannan duniyar tamu Allah madaukaki ya ce: alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5)
Amsa: Sai ka ce: Su basa amsawa ga wanda ya kira su, kuma basu da iko bisa amsawa wanda ya kira su ko ya nemi agajin su, Allah madaukaki ya ce: : Kuma wadanda kuke kira wanda ba shi ba, ba su mallakar ko bawon kwallon dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun ji ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafircewa shirkarku. (Faadir:13-14). Yaa tabewar wanda shaidanu da masu kira zuwa bata suka yaudare shi ! sai gashi sun kawata masa rokon matattu da wadanda ke cikin kabur-bura daga annabawa da waliyyai da salihan bayi, Allah madaukaki ya ce : Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu
Amsa: Sai ka ce: wan nan Babbar shirka ce saboda fadin sa madaukaki : Kayi salla ga ubangijin ka kuma ka yi yanka. (Al-kauthar:2). Da fadar sa madaukaki: Ka ce : lallai ne salla ta da yanka na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne ubangijin halitta. Babu abokin tarayya a gareshi, kuma da wancan ne aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa. (Al-an`aam: 162-163). Da fadin sa manzon Allah mai tsira da aminci- (Allah ya la`anci wanda yayi yanka ga wanin Allah) muslimu ne ya rawaito.
Kuma ka`ida tana cewa: (Duk abin da ya kasance aiwatar da shi zuwa ga Allah ibada ne, to aiwatar da shi zuwa ga wanin Allah shirka ne)
Amsa: sai ka ce: Yana daga babbar shirka saboda fadar sa mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi: (Duk wanda yayi bakance zai yiwa Allah biyayya to lallai ne ya yimasa da`ar, kuma duk wanda ya yi bakancen zai sabawa Allah to kada ya kuskura ya saba masa) Bukhari ne ya rawaito. To bakance wata ibada ce ta Magana ko dukiya ko yi da jiki, gwargwadon yadda mai yin bakance ya ke yin bakancen, shi ne lizimtawa kai abinda bai zama wajibi akan sa a shar`ance ba domin kaunar samun abinda ake nema ko ije wani abin tsoro ko godiya ga wata ni`ima, da ta faru ko wata azaba da ta gushe, su wadannan suna daga cikin ibadun nan da bai halasta a aiwatar da su ga wanin Allah ba. Saboda Allah ya yi yabo ga masu cika alkawarin bakance , Allah madaukaki ya ce: Suna cikawa da alwashin bakancen da suka dauka, kuma suna tsoron wani yini wanda sharrin say a kasance mai tartsatsi ne. (Al`insan: 7)
Kuma ka`ida tana cewa : Dukkan aikin da Allah ya yi yabo akan mai aikata shi to shi mai shiga ne cikin ayyukan ibada, duk abin da kuma ya kasance Ibada ne to aiwatar da shi ga wanin Allah shirka ne.
Amsa: Sai ka ce: Amsar tana bayyana ne ta hanyar sanin nau`ikan :neman tsari guda uku su ne
- Neman tsari na tauhidi kuma na ibada: shi ne neman tsari da Allah daga dukkanin abin da kake jin tsoro, Allah Madaukaki ya ce:Ka ce: ina neman tsari ga ubangijin Mutane, mamallakin mutane, abin bautawar mutane, Daga sharrin mai sanya wasuwasi a cikin kirazan mutane, Daga Aljannu da Mutane.
- Neman tsari wanda aka halasta: Shi ne neman tsari da abin halitta wanda yake a raye a gaban ka yana da iko cikin abin da aka kaddara zai iya aiwatarwa bisa abin da ya kasance abin kaddarawa ne a shari`ance, manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (Duk wanda ya sami wata mafaka ko wata matsara to ya yi aiki da ita) muslimu ne ya rawaito
3 Neman tsari na shirka: Shi ne neman tsari ga wanin Allah a cikin abin da babu mai kio akan sa sai Allah, Allah madaukaki ya ce: (Kuma lallai ne shi cewa wasu maza daga cikin mutane, sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, saboda haka sai suka kara musu girman kai. (Al-jinni: 6)
Amsa / Sai ka ce: Zan fadi abin da manzon Allah mai tsira da aminci ya shiyar da ni zuwa gareshi- ya ce: (Duk wanda ya sauka wani masauki sai ya ce: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin nashi). Muslim ne ya Rawaito
Amsa: Sai ka ce: Wan nan yana daga babbar shirka mai ruguza ayyuka mai fitarwa daga addini mai kaiwa ga halaka dauwamammiya ta har abada ga wanda ya afaka cikin sa kuma bai tuba daga gareshi ba kafin mutuwa, saboda fadin Allah madaukaki: Ko wanene yake amsawa mai tsananin bukata idan ya kira shi, kuma ya yaye masa bakin cikin (an-namli: 62). Yana nufin babu mai amsa masa sai Allah kuma babu mai yaye masa damuwa sai Allah, sai Allah tsarkakakken sarki ya zargi wanda ke neman agajin wanin sa da sigar tambaya saboda shi neman agaji da neman taimako ga Allah ibada ne, Allah madaukaki ya kuma fada: Ku tuna yayin da kuke neman agajin ubangijin ku. (al-anfal: 9). Kuma hakika ya tabbata a cikin littafin sahihul bukhari daga abi hurairata Allah ya masa yadda, cewa annabi mai tsira da aminci ya ce: (Kada na sami dayan ku ya zo ranar alkiyama alhali ya dauko rakumi akan wuyan sa yana kukan rakuma sai ya ce: ya manzon Allah ka agajeni, sai na ce masa: hakika na isar maka da sako, don haka ba na mallakar komai a gareka daga Allah, kada na sami dayan ku ya zo ranar kiyama akan wuyan sa yana dauke da doki yana ta haniniya, sai ya ce: ya manzon Allah ka agajeni, sai na ce: bani mallakar komai a gareka daga Allah hakika na isar maka da sako) Bukhari da muslimu sun fitar da shi. Kuma sanannen abu ne cewa ya halasta a garemu da munemi agajin wanda yake rayayye ne kuma munagin shi gamu-ga-shi, ba wanda baya nan ba, kuma wannan ya halasta ne cikin abin da yake da iko akan sa, neman agaji ga abin halitta rayayye yana nufin neman taimako daga gareshi cikin abin da dan`adam yake da ikon yin sa, kamar yanda abokin annabi musa ya nemi taimakon annabi musa amincin Allah ya tabbata a gareshi akan makiyin su, Allah madaukaki ya ce: Sai wannan da yake daga jama`ar sa ya nemi agajin sa akan wannan da yake daga makiyan sa. (Al-qasas:15). Amma neman agajin wadanda basu nan daga mutane da aljannu da ma`abota kabur-bura, sai limaman malamai suka hadu akan bacin sa da haramcin sa da kuma cewa hakan yana daga shirka
Amsa/ sai ka ce: Bai halatta ba, ta yanda dukkanin limaman malamai sun hadu bisa haramcin dukkanin sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah, kuma yana wajaba da a canza sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah kamar Abdun-nabiyi, ko Abdur-rasuli, ko Abdul-Husaini, ko Abdulka`abati (Bawan ka`aba) da wanin su daga sunayen bautarwa ga wanin Allah madaukaki . kuma mafi soyuwar sunaye a wurin Allah sune: (Abdullahi, da kuma Abdur-rahman) kamar yadda yake cikin hadisi daga manzon Allah mai tsira da aminci : (Hakika mafi soyuwar sunanye a wurin Allah (sune) Abdullahi da Abdur-rahman) Muslimu ne ya rawaito. Kuma yana wajaba a canza sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah wannan kuma ya rataya ne ga wadanda suke a raye ana kiran su da sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah
Amsa/ sai ka ce: Wannan yana daga shirka saboda fadin sa mai tsira da aminci-: (Wanda ya rataya laya hakika yayi shirka) Ahmad ne ya rawaito a cikin musnadin sa, da kuma fadin sa mai tsira da aminci -: (Babu wani maratayi mai wutiri da zai wanzu a wuyan rakumi ko wani maratayi na daban fa ce sai na yanke shi) Bukhari ne ya rawaito. Da fadin sa mai tsira da aminci : (Wanda ya kulla gemun sa ko ya rarrataya wutiri, ko ya yi tsarki da kashin dabbobi ko wani kashi to hakika annabi Muhammad (mai tsira da aminci) ya barrantu daga gareshi) Ahmad ne ya rawaito shi. Da kuma fadin sa mai tsira da aminci: (Hakika tofe-tofe da layu da kuma guru shirka ne) Abu Dawud ne ya rawaito shi. Da kuma fadin sa mai tsira da aminci : (Duk wanda ya rataya laya to kada Allah ya cika masa burin sa) Ibn Hibban ne ya rawaito a cikin sahihin sa. Kuma duk wanda ya rataya al-amuran sa da rudani da kuma tatsuniyoyi hakika ya tabe, Ya zo cikin hadisi : (Wanda duk ya rataya da wani abu to an kyale shi da wannan abin)
Abin nufi da At-tiwala: wani tsafi ne da ake yin sa suna kudurtar cewa yana sanya soyuwar miji ga matar sa ko kuma yana raba tsakanin su, kuma suna yin amfani da shi wurin jefa gaba a tskanin masoya da kuma makusanta na jini
Abin nufi da At-tama`im: wani abune da ake ratayawa kananan yara saboda tunkude musu kambin baka ko Hassada
Kuma ma`anar Laya, Imamul munziri ya ce: (Wani rufi ne na fata da aka dinke shi da zare da allura, su kasance su rataya ta suna ganin cewa ita zata tunkude musu aibubbuka), wannan kuma jahilci ne da bata, saboda ba sababi ba ce a shar`ance ko a kaddarance, kuma wannan ya hada da sanya kambu da kuma rataya tsumma da kuma makarai ga mutum, da dabbobi, da mota, da kuma gida
Amsa/ sai ka ce : Neman tabarruki kasha biyu ne
- Neman tabarraki shar`antacce, Kur`ani da sunna sun yi nuni bisa shar`antuwar sa da kuma amfanuwar mai aikata shi da shi, kuma baya halatta a kudurci neman Albarka a cikin komai sai idan da dalili daga kur`ani da sunna babu wata dama da za`a shigar da hankali ko kyautata zato a cikin ta, bamu iya sanin cewa wannan abin akwai albarka ko da akwai albarka a cikin sa sai da labari daga mahalicci gwani mai albarkar suna da daukaka, ko daga manzon sa mai tsira da aminci, kuma albarka da alheri dukkanin su suna cikin biyayyar kur`ani da hadisi, daga cikin su ne muke sanin abubuwan da suke da albarka da kuma yadda zamu yi tabarraki da su kamar neman tabarraki da zatin Manzon Allah mai tsira da aminci- da abin da ya rabu daga gareshi na yawu da kuma gashi, da abin da yake like da jikin sa na tufafi, wannan kuma kebantacce ne da shi mai tsira da Aminci- da kuma duk abin da ya tabbata yana da alaka da shi, daga ciki akwai gashi da tufafi, kuma ma`abota tatsuniya suna yin karya suna riya cewa akwai wani daga cikin gashin sa a wurin su, da wani tufafi daga tufafin sa, duk wannan suna yi ne domin wasa da hankulan wasu daga cikin Musulamai, da kuma bata musu Addinin su, da karbe musu abin Duniya
Kashi na biyu: Neman Tabarrukin da aka haramta, wanda yake kai Mutum zuwa ga Shirka kamar naiman Tabarruki da Zatin Mutanen kirki da kuma abinda yake futa daga cikinsu, da neman tabarruki da Kaburburansu da Sallah da yin Addu'a a wurinsu, da kuma neman Albarka da Kasarta da kudurcewa wannan Magani ne, kwatan kwacinsa neman Albarkarka ko Dawafi ko Rataya musu wani kyalle a wani guri ko Dutse ko wata Bishiya da ake canfa Albarkarta, kuma hakika babu wani abu da aka shar'anta Sunbantarsa ko shafarsa sai Hajarul Aswad da ke Ka'aba da Rukunanta kuma bayanta Haramun ne a shafi wani abu ko a sunbance shi ko ayi masa Dawafi, kuma wannan shirka ce Babba ga wanda ya Kudurce cewa yana bada Albarka a zatinsa ko kuma yana daga cikin Karamar Shirka ga wanda ya canfa cewa wannan shi Sababin samun Albarka.