Skip to content

Idan aka ce dakai nawa ne rabe-raben shirka

السؤال

Tambaya: Idan aka ce dakai nawa ne rabe-raben shirka

الجواب

Amsa: Kace kashi biyu ce:

1.Shirka babba: Ita ce juyar da wani nau’I na ibada zuwa ga wanin Allah, kamar dogaro ga wanin Allah, ko neman taimako daga matattu, ko yin yanka don wanin Allah, ko bakance ga wanin Allah, ko sujjada da neman agaji daga wanin Allah a abin da babu mami iya yinsa sai Allah, kamar neman agaji daga wanda ba ya nan ko matacce babu wanda zai yi wannan jahilcin sai wanda ya qudurce cewa za su iya amsa masa addu’arsa, kuma za su iya aikata abin da babu wanda zai iya sai Allah. To wannan ya xorawa abin halitta siffofin ubangiji, don haka sai ya qasqantar da kai gare shi,kuma ya wulaqanta gare shi irin wulaqantar bauta, ya zama yana dogaro akansa, yana neman agajinsa da kiransa yana roqonsa abin da wani halitta da zai iya yinsa. Wannan ya isa abin mamamki a ce wai a nemi agaji da gajiyayye, wanda ba zai iya cutar da kansa ko ya amfanar da shi da komai ba, bai mallaki mutuwa ko rayuwa ko tashi ba, wanda ba zai iya hana cuta ta same shi ba yaya zai iya hana tag a waninsa, misalin wannan shi ne kamar wanda ruwa ya ciwo ne ya dinga neman taimako daga wanda shima ruwan ya ciwo shi, Allah sarki! Amma ta yaya basirar wasu take shafewa, hankulansu su tafi, har su dinga aikata irin wannan shirka da ta savawa sharia, ta savawa hankali ta ci karo da abin da shi ne haqiqa.

2 Shirka qarama: itace kamar ‘yar qaramar riya. Manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace mafi girman abin da nake jiye muku tsoronsa shine qaramar shirka. Da aka tambaye shi sai yace ita ce riya (Muslim ne ya ruwaito shi). Hakanan kamar rantsuwa da wanin Allah. Kamar yadda Manzon Allah tara da amincin Allah yace duk wanda ya rantse a wanin Allah to ya kafirta ko yayi shirka Tirmizi ne ya rawaito).