Idan aka ce da kai waxanne ne sharuddan karvar aiki a wajen Allah.
السؤال
Tambaya: Idan aka ce da kai waxanne ne sharuddan karvar aiki a wajen Allah.
الجواب
Amsa: Sai ka ce Allah ba ya karvar aiki har sai ya cika sharaxai biyu, na farko aikin ya zama don Allah a ka yi shi, don Allah yace ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu karkacewa vata. (Bayyinah 5) da faxina Maxaukakain Sarki “Duk wanda yake fatan ya gamu da Allah (lafiya) to sai ya aikata aiki mai kyau kuma kada ya haxa kowa da Allah a ibada (Kahfi 110).
Sharadi na biyu shi ne lallai aikin ya dace da shari’ar da manzon Allah tsira da amincin Allah ya zo da ita. Kuma dalilin haka shine faixn Allah mai girma ka ce (musu) idan dai kuna son Allah to ki yi biyayya a gare ni, sai Allah ya so ku. (Ali Imran 31).Da kuma faxin manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi “duk wanda ya aikata aikin da babu umarnin mu a cikinsa to za a juyar masa da shi” (Muslim ne ya rawaito shi) don haka idan aiki ai dace da shiryarwar manzon Allah tsira da amincin a gare shi ba to ba za a karva ba ko da kuwa mai yinsa ya tsarkake niyyarsa.