Idan aka ce da kai : menene abubuwan da suke warware musulunci ?
السؤال
Tambaya / Idan aka ce da kai : menene abubuwan da suke warware musulunci ?
الجواب
Sai ka ce : Mai warwarewa shi ne mai lalatawa kuma mai batawa , duk lokacin da ya hau kan wani abu zai lalata shi kuma zai bata shi , kamar abubuwan da suke warware alwala wadanda daga aikata su alwalar sa ta lalace, kuma dole ne ya sake maimaita ta , kwatankwacin su ne irin abubuwan da suke warware musulunci wadanda idan bawa ya aikata su to musuluncin sa ya baci ya lalace, mai aikata su kuma ya fice daga kwaryar musulunci zuwa kafirci , kuma hakika malamai sun ambaci nau`ika da yawa a cikin babuka na ridda da hukuncin mai yin ridda daga abubuwan da za su iya fitar da musulmi daga addinin sa kuma jinin sa da dukiyar sa su halasta, kuma mafi hadarin su mafi girmansu da mafi yawan wanda suka fi faruwa, da wanda malamai suka hadu akan su; su ne masu warwarewa guda goma : Na farkon su : Yin shirka a cikin bautawa Allah madaukaki, Allah madaukaki ya ce: Lallai ne Allah baya gafarta ayi shirka da shi, kuma yana gafarta abinda ya ke bayan wannan, (an-nisa`I : 116). Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: Lallai ne shi wanda ya yi shirka da Allah to tabbas Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomar sa wutam kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai. (al-ma`ida: 72.). yana daga abinda ke warware musulunci shi ne kiran wanin Allah, da neman agaji da kuma neman tsarin su, da yin bakance da yin yanka a garesu kamar wanda zai yiwa aljani yanka ko ga wani kabari, ko ga wani waliyyi rayayye ne ko matacce domin neman janyo wani alheri ko tunkude wata cutuwa kamar yanda jahilai wadanda aka yaudare su da karyace-karyace da shubuhohin shaidanu batattu suke aikatawa.
Na biyu : Wanda ya sanya wani tsani tsakanin sa da tsakanin Allah yana rokar su, yana kuma rokon su ceto, yana kuma dogaro da su cikin neman biyan bukatun sa da abubuwan da yake so na duniya da lahira, to hakika ya kafirta da ijima`in malamai. Allah madaukaki ya ce: Kuma ka ce: kadai ni ina kiran ubangiji na kuma ba na hada shi da kowa a bauta. ( Al-jinn: 20)
Na uku : Duk wanda bai kafurtar da mushirikai ba , ko ya yi kokwanto a cikin kafircin su, ko yake ganin ingancin hanyar da suke tafiya akanta, to ya kafurta, Allah madauakaki ya ce: Kuma yahudawa suka ce: Uzairu dan Allah ne, kuma nasaara suka ce masihu dan Allah ne, wancan zancen su ne da bakunan su, suna kama da maganar wadanda suka kafirta gabanin su, Allah ya la`ance su , ta yaya aka karkatar da su. (Suat Attauba: 30). Saboda yadda da kafirci shima kafirci ne, kuma addini baya ingantuwa sai da kafircewa dagutu ta hanyar kudurce bacin duk addinin da ba na musulunci ba da yin gaba da shi, da kaurace masa da kuma kauracewa ahalinsa, da yakar su gwargwadon iko.
Na hudu : Duk wanda ya kudurce cewa wanin shiryarwar annabi mai tsira da aminci ta fi shiryarwar sa cikar kamala, ko kuma cewar Hukumcin wanin sa ya fi nasa hukumcin kyautatuwa, kamar wanda ya ke fifita hukumcin dagutai da kuma tsarin dokokin da mutane suka kirkiroma kansu da hukumce-hukumcen su akan hukumcin Allah da manzon sa, Allah madaukaki ya ce: To a`aha ! Ina ratsuwa da ubangijin ka, ba za su yi imani ba sai sun yadda da hukuncin ka cikin abin da ya saba a tsakanin su, sa`annan kuma basu sami wanu kunci a cikin zukatan su ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama cikakkiyar sallamawa. (an-nisa`i : 65). Kuma duk wanda ya gabatar da darikun shehunnan bata da abubuwan da suka kago da bidi`o`insu akan ingantacciyar sunna alhali yana sane cewa ita sunnar annabi ce, duk wanda ya aikata wannan to shi kafiri ne da Haduwar malamai
Na biyar : Wanda duk ya fusata da wani abu daga cikin abinda manzon Allah mai tsira da aminci ya zo da shi ko da ya yi aiki da shi to hakika ya kafurta, Allah madaukaki ya ce : Wannan saboda cewa lallai su, sun ki abin da Allah ya saukar, domin haka ya bata ayyukan su. ( Suarat Muhammad: 9
Na shida : wanda duk ya yi Izgili da wani abu na daga addinin manzon Allah mai tsira da aminci- kamar wanda yake yin izgilanci da sashin Hukunce-hukuncen sa da shari`o`in sa da sunnonin sa ko abinda ya bada labarin su, ko kuma ya rika izgilanci da abin da Allah ya tanadar da shi na daga lada ga masu yi masa da`a, ko kuma ukubar da ya tanadar ga masu sabo daga abinda Allah da manzon sa mai tsira da Aminci suka bada labari gameda shi to hakika ya kafirta, dalili kuwa shi ne fadin Allah madaukaki : ka ce shin da Allah da ayoyin sa da manzon sa kuka kasance kuna yiwa izgilanci? Kada ku kawo wani uzuri hakika kun kafirta a bayan imanin ku. (Suat Tauba: 65-66.)
Na bakwai : Sihiri, kuma baya kasancewa sai ta hanyar amfani da aljanu da shaidanu da kuma yin tarayya da su da aikata ayyukan kafirci domin neman yaddar su , daga ciki akwai jujjuyawa da tausasawa mai tasiri a cikin jikkunan mutane, da kuma cikin hankulan su, duk wanda ya aikata shi ko ya yadda da shi to hakika ya kafirta, dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : kuma basu sanar da kowa har sai sun ce : mu fitina ce kawai, saboda haka kada ka kafirta. (Suat Al-bakara:102).
Na takwas : Taimakawa mushirikai da kuma yin taimakekeniya da su, da taimakon su wajen cin Nasara akan Musulmai, dalili kuwa shi ne fadin sa Allah madaukaki : Kuma wanda ya jibince su daga gare ku, to lallai ne shi yana daga gare su, lallai Allah baya shiriyar da mutane azzalumai. (Suat Al-ma`ida : 51).
Na tara : Wanda duk ya kudurci cewa wasu sashin mutane zasu iya fita daga karkashin shari`ar annabi Muhammad mai tsira da aminci- kamar yadda ya yalwaci khidr ficewa daga shari`ar annabi musa amincin Allah ya tabbata a gareshi to shi kafiri ne saboda fadar Allah madaukaki : Duk wanda ya nemi wani addinin da ba na musulunci ba to baza a karba daga gareshi ba kuma shi a lahira yana daga cikin asararru . (Suat Alil-imrana: 85)
Na goma: Bijirewa daga Addinin Allah (musulunci), baya koyar sa kuma baya aiki da shi, dalili kan haka fadin sa Allah madaukaki: Kuma wanene yafi zalunci bisa ga wanda aka tunantar da ayoyin ubangijin sa, sa`annan ya bijire daga barin su, lallai mu masu daukar fansa ne daga masu laifi. (As-sajdah : 22) . Abin nufi da bijirewa daga addinin Allah shi ne : Rashin koyon abin da ya zamar masa dole na daga abinda Addinin sa baya ingantuwa sai da sanin shi daga ginshikan Addininsa
Bayan ambaton wadannan abubuwan masu warware musulunci; ya kyautu a garemu da mu yi tambihi guda biyu masu muhimmanci su ne :
- Cewa Amabaton wadan nan abubuwa masu warware musulunci domin a tsorata daga garesu, kuma a tsoratar da mutane da su guje su, domin shedanu da mataimakan su masu gurbatar hankali masu batarwa suna zaman dako wajen hana musulmi bin hanya mai kyau, sai su ribaci sakacin wasu daga cikin su kuma su ribaci jahilcin su domin su fitar da su daga cikin kwaryar gaskiya zuwa batacciyar hanya, kuma domin su juyar da su ga barin hanyar aljanna zuwa wuta
- Cewa saukar da wadan nan abubba masu warware Addini bisa hakikanin yadda suke yana daga aikin manyan malamai masu zurfi cikin ilimi, sune wadanda suke sanin dalilai da hukunce-hukunce da kiyayewa ga saukakken hukunce-hukuncen da ke kan mutane, ba kowa ne yin hakan yake halasta a gareshi ba