Skip to content

Idan aka ce da kai: Waye yake gudana da Mulkin Sammai da Kasa da abinda ke tsakaninsu?

السؤال

Tambaya: Idan aka ce da kai: Waye yake gudana da Mulkin Sammai da Kasa da abinda ke tsakaninsu?

الجواب

Amsa/ sai ka ce: wanda ke jijjuya al-amarin sammai da kasa da wadanda ke cikin su da abinda ke tsakanin su shi ne Allah shi kadai ne ba shi da abokin tarayya, babu wani mamallakin da ba shi ba, kuma ba shi da abokin tarayya babu mai taimakon sa kuma babu mataimaki a gareshi, tsarki da godiya sun tabbata a gareshi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ka ce: ku kirayi wadanda kuka riya (cewa abubuwan bautawa ne) ba Allah ba, ba sa mallakar kwatankwacin kwayar zarra a cikin sammai kuma basa mallakarsa a cikin kasa, kuma basu da wani rabon tarayya a cikin su (sammai da kasa) kuma ba shi da wani mataimaki daga garesu. (saba`a: 22)