Skip to content

Idan aka ce da kai : shin za`a iya yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda ya aikata sabo?

السؤال

Tambaya/ Idan aka ce da kai : shin za`a iya yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda ya aikata sabo?

الجواب

Amsa/ Sai a ce: ba`a yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda aikata zunubai da sabo ko da kuwa manya ne, matukar dai basu daga cikin lafuka masu kafirtarwa wadanda nassoshin shari`a na cikin kur`ani da sunna suka yi nuni a kansu kuma Sahabbai da manyan malamai suka fadesu , zai zamo akan imanin sa kuma ya kasance daga masu sabo na ahalin tauhidi matukar bai afka cikin babban kafirci ko babbar shirka ko kuma babban Munafurci ba