Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta
Daga Madar Dan Ukamis - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta".
«إِذَا قَضَى اللَّهُ لِعَبْدٍ أَنْ يَمُوتَ بِأَرْضٍ جَعَلَ لَهُ إِلَيْهَا حَاجَةً».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah idan Ya hukunta Ya kuma kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa alhali shi ba ya cikin kasar; sai a sanya masa wata bukata gareta sai ya tafi kasar, sai a karbi ransa a cikinta.
...:
Hadisin gasgatawa ne ga fadin Allah - Mai girma da daukaka -: {Kuma wata rai ba ta sanin a wacce kasa zata mutu}.
Sunan Tirmizi (4/ 23) (2146).
Kari (1)
تحفة الأحوذي (6/ 299).