Skip to content
Jerin Surori /

المُرسَلات

المُرسَلات is chapter 77 of the Quran and has 50 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

50 Ayoyi Lambar Sura 77
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا

Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.

فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا

Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.

وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا

Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.

فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا

sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.

فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا

Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.