Skip to content
Jerin Surori /

الحِجر

الحِجر is chapter 15 of the Quran and has 99 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

99 Ayoyi Lambar Sura 15
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ

A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.

رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ

Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.

Explanation & meanings · 1
  1. Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa.

ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ

Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.

مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ

Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.