Skip to content

Idan aka ce da kai: Menene wannan abin da akeji a wasu lokuta a wasu daga cikin kabur-buran matattu wadanda jahilai ke girmama su?

السؤال

Tambaya: Idan aka ce da kai: Menene wannan abin da akeji a wasu lokuta a wasu daga cikin kabur-buran matattu wadanda jahilai ke girmama su?

الجواب

Amsa: Sai ka ce: Su wadan nan Muryoyin Shaidanun Aljanu ne, suna Rudar Jahilai da cewa wannan sautin ma`abicin kabarin ne ta yadda har sai sun fitinance su sun cakuda musu addinin su sun batar da su, alhali su ma`abota kabarin basa ji kuma basa amsawa ga wanda yake rokon su ko mai kiran su da nassin kur`ani mai girma, Allah madaukaki ya ce: Hakika lallai ne kai baka jiyar da matattu.(An-namli: 80). Allah madaukaki ya kuma cewa: Idan kun kira su basa jin kiran naku. (Fadir: 14) Allah madaukaki ya kuma fada: Kuma kai ba mai jiyar da wadanda ke cikin kabur-bura ba ne.(Fadir: 22) To ta yaya za su amsa musu alhali su suna wata duniyar ta barzahu, basu da wata alaka da ahalin wannan duniyar tamu Allah madaukaki ya ce: alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5)