Skip to content

To idan aka ce da kai: Menene hukuncin yin yanka ga wanin Allah domin neman kusanci ga wanda aka yiwa yankan?

السؤال

Tambaya/ To idan aka ce da kai: Menene hukuncin yin yanka ga wanin Allah domin neman kusanci ga wanda aka yiwa yankan?

الجواب

Amsa: Sai ka ce: wan nan Babbar shirka ce saboda fadin sa madaukaki : Kayi salla ga ubangijin ka kuma ka yi yanka. (Al-kauthar:2). Da fadar sa madaukaki: Ka ce : lallai ne salla ta da yanka na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne ubangijin halitta. Babu abokin tarayya a gareshi, kuma da wancan ne aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa. (Al-an`aam: 162-163). Da fadin sa manzon Allah mai tsira da aminci- (Allah ya la`anci wanda yayi yanka ga wanin Allah) muslimu ne ya rawaito.

Kuma ka`ida tana cewa: (Duk abin da ya kasance aiwatar da shi zuwa ga Allah ibada ne, to aiwatar da shi zuwa ga wanin Allah shirka ne)