to idan aka ce da kai: Shin ya halasta a bautar da sunaye ga wanin Allah kamar (ace) Abdun-nabiyi ko Abdul-husaini da kuma kwatankwacin haka?
السؤال
Tambaya/ to idan aka ce da kai: Shin ya halasta a bautar da sunaye ga wanin Allah kamar (ace) Abdun-nabiyi ko Abdul-husaini da kuma kwatankwacin haka?
الجواب
Amsa/ sai ka ce: Bai halatta ba, ta yanda dukkanin limaman malamai sun hadu bisa haramcin dukkanin sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah, kuma yana wajaba da a canza sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah kamar Abdun-nabiyi, ko Abdur-rasuli, ko Abdul-Husaini, ko Abdulka`abati (Bawan ka`aba) da wanin su daga sunayen bautarwa ga wanin Allah madaukaki . kuma mafi soyuwar sunaye a wurin Allah sune: (Abdullahi, da kuma Abdur-rahman) kamar yadda yake cikin hadisi daga manzon Allah mai tsira da aminci : (Hakika mafi soyuwar sunanye a wurin Allah (sune) Abdullahi da Abdur-rahman) Muslimu ne ya rawaito. Kuma yana wajaba a canza sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah wannan kuma ya rataya ne ga wadanda suke a raye ana kiran su da sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah