Skip to content

Idan akace da kai : Shin ita walittaka kebantacciya ce a cikin wani sashi na Muminai ban da wasu?

السؤال

Tambaya / Idan akace da kai : Shin ita walittaka kebantacciya ce a cikin wani sashi na Muminai ban da wasu?

الجواب

Amsa: Sai ka ce: Duk wanda ya kasance mumini mai tsoron Allah to shi waliyyi ne a wurin Allah, dalilin haka fadin sa Allah madaukaki: To, lallai ne masoyan Allah babu tsoro a kansu, kuma baza su kasance suna yin bakin ciki ba, Wadanda suka yi imani kuma suka kasance suna yin takawa. (Yunus: 62-63). Ba kebantacciya ba ce ga wani daga cikin muminai banda wani, saidai matakan ta suna tserewa juna (wani yana iya fin wani), kuma takawa tana nufin: aikata abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi umurni da kuma nisantar abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi hani ga barinsa, kuma kowane mumini yana da walittaka gwargwadon imanin sa da Biyayyarsa.