Skip to content

Idan aka ce da kai: Shin wadan da ba annabawa ba daga waliyyai kubutattu ne daga aikata manya da kananan laifuka?

السؤال

Tambaya / Idan aka ce da kai: Shin wadan da ba annabawa ba daga waliyyai kubutattu ne daga aikata manya da kananan laifuka?

الجواب

Amsa/ Sai ka ce: Duk wanda ya kasance waliyyi ba daga cikin annabawa ba to shi ba kubutacce ba ne daga afkawa cikin kanana da manyan laifuka, hakika hakan ya faru ba sau daya ko sau biyu ba daga manyan waliyyai da salihan bayi wasu daga cikin zame-zame da tuntube da zurme-zurme, saidai cewa su suna gaggauta tuba da komawa ga Allah, sai Allah ya gafarta musu