Idan aka ce da kai: Shin neman tabarraki nau`i daya ne ko sama da haka ne?
السؤال
Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin neman tabarraki nau`i daya ne ko sama da haka ne?
الجواب
Amsa/ sai ka ce : Neman tabarruki kasha biyu ne
- Neman tabarraki shar`antacce, Kur`ani da sunna sun yi nuni bisa shar`antuwar sa da kuma amfanuwar mai aikata shi da shi, kuma baya halatta a kudurci neman Albarka a cikin komai sai idan da dalili daga kur`ani da sunna babu wata dama da za`a shigar da hankali ko kyautata zato a cikin ta, bamu iya sanin cewa wannan abin akwai albarka ko da akwai albarka a cikin sa sai da labari daga mahalicci gwani mai albarkar suna da daukaka, ko daga manzon sa mai tsira da aminci, kuma albarka da alheri dukkanin su suna cikin biyayyar kur`ani da hadisi, daga cikin su ne muke sanin abubuwan da suke da albarka da kuma yadda zamu yi tabarraki da su kamar neman tabarraki da zatin Manzon Allah mai tsira da aminci- da abin da ya rabu daga gareshi na yawu da kuma gashi, da abin da yake like da jikin sa na tufafi, wannan kuma kebantacce ne da shi mai tsira da Aminci- da kuma duk abin da ya tabbata yana da alaka da shi, daga ciki akwai gashi da tufafi, kuma ma`abota tatsuniya suna yin karya suna riya cewa akwai wani daga cikin gashin sa a wurin su, da wani tufafi daga tufafin sa, duk wannan suna yi ne domin wasa da hankulan wasu daga cikin Musulamai, da kuma bata musu Addinin su, da karbe musu abin Duniya
Kashi na biyu: Neman Tabarrukin da aka haramta, wanda yake kai Mutum zuwa ga Shirka kamar naiman Tabarruki da Zatin Mutanen kirki da kuma abinda yake futa daga cikinsu, da neman tabarruki da Kaburburansu da Sallah da yin Addu'a a wurinsu, da kuma neman Albarka da Kasarta da kudurcewa wannan Magani ne, kwatan kwacinsa neman Albarkarka ko Dawafi ko Rataya musu wani kyalle a wani guri ko Dutse ko wata Bishiya da ake canfa Albarkarta, kuma hakika babu wani abu da aka shar'anta Sunbantarsa ko shafarsa sai Hajarul Aswad da ke Ka'aba da Rukunanta kuma bayanta Haramun ne a shafi wani abu ko a sunbance shi ko ayi masa Dawafi, kuma wannan shirka ce Babba ga wanda ya Kudurce cewa yana bada Albarka a zatinsa ko kuma yana daga cikin Karamar Shirka ga wanda ya canfa cewa wannan shi Sababin samun Albarka.