Skip to content

Idan aka ce da kai: Shin zamu iya neman tsari da wanin Allah Madaukaki ?

السؤال

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin zamu iya neman tsari da wanin Allah Madaukaki ?

الجواب

Amsa: Sai ka ce: Amsar tana bayyana ne ta hanyar sanin nau`ikan :neman tsari guda uku su ne

  1. Neman tsari na tauhidi kuma na ibada: shi ne neman tsari da Allah daga dukkanin abin da kake jin tsoro, Allah Madaukaki ya ce:Ka ce: ina neman tsari ga ubangijin Mutane, mamallakin mutane, abin bautawar mutane, Daga sharrin mai sanya wasuwasi a cikin kirazan mutane, Daga Aljannu da Mutane.
  2. Neman tsari wanda aka halasta: Shi ne neman tsari da abin halitta wanda yake a raye a gaban ka yana da iko cikin abin da aka kaddara zai iya aiwatarwa bisa abin da ya kasance abin kaddarawa ne a shari`ance, manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (Duk wanda ya sami wata mafaka ko wata matsara to ya yi aiki da ita) muslimu ne ya rawaito

3 Neman tsari na shirka: Shi ne neman tsari ga wanin Allah a cikin abin da babu mai kio akan sa sai Allah, Allah madaukaki ya ce: (Kuma lallai ne shi cewa wasu maza daga cikin mutane, sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, saboda haka sai suka kara musu girman kai. (Al-jinni: 6)