Idan aka ce da kai: Shin waliyyai da wadansun su suna amsawa ga wanda ke neman agajin su da kuma neman taimako daga wajen su ?
السؤال
Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin waliyyai da wadansun su suna amsawa ga wanda ke neman agajin su da kuma neman taimako daga wajen su ?
الجواب
Amsa: Sai ka ce: Su basa amsawa ga wanda ya kira su, kuma basu da iko bisa amsawa wanda ya kira su ko ya nemi agajin su, Allah madaukaki ya ce: : Kuma wadanda kuke kira wanda ba shi ba, ba su mallakar ko bawon kwallon dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun ji ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafircewa shirkarku. (Faadir:13-14). Yaa tabewar wanda shaidanu da masu kira zuwa bata suka yaudare shi ! sai gashi sun kawata masa rokon matattu da wadanda ke cikin kabur-bura daga annabawa da waliyyai da salihan bayi, Allah madaukaki ya ce : Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu