Skip to content
Jerin Surori /

الأنعَام

الأنعَام is chapter 6 of the Quran and has 165 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

165 Ayoyi Lambar Sura 6
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ ٱلظُّلُمَٰتِ وَٱلنُّورَۖ ثُمَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡ يَعۡدِلُونَ

Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa.

Explanation & meanings · 1
  1. Duffai na dare da zãlunci da bin hukunce-hukuncen al'ãdu, haske kuma shĩ ne na taurãri da wuta da shari'u na Littãfi da annabci.

هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن طِينٖ ثُمَّ قَضَىٰٓ أَجَلٗاۖ وَأَجَلٞ مُّسَمًّى عِندَهُۥۖ ثُمَّ أَنتُمۡ تَمۡتَرُونَ

Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurin Sa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka.

وَهُوَ ٱللَّهُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَفِي ٱلۡأَرۡضِ يَعۡلَمُ سِرَّكُمۡ وَجَهۡرَكُمۡ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُونَ

Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa.

وَمَا تَأۡتِيهِم مِّنۡ ءَايَةٖ مِّنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِمۡ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ

Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa.

فَقَدۡ كَذَّبُواْ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ فَسَوۡفَ يَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.