Skip to content
Al'an'am /

Aya 137

6 : 137

Aya 137 of Al'an'am (6 : 137). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'an'am Ayoyi 165
Sura · Al'an'am
Hausa · Gummi
6 : 137

وَكَذَٰلِكَ زَيَّنَ لِكَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ قَتۡلَ أَوۡلَٰدِهِمۡ شُرَكَآؤُهُمۡ لِيُرۡدُوهُمۡ وَلِيَلۡبِسُواْ عَلَيۡهِمۡ دِينَهُمۡۖ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ

Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Sunã turbuɗe 'ya'ya mata, dõmin tsõron talauci kõ dõmin tsõron kunya. Sai mai haihuwa ta haihu a bãkin rãmi, idan mace ta haifa, sai ta tũra ta cĩkin rãmin ta rufe, idan kuma namiji ne sai ta bar shi. Haka kuma kashe 'ya'ya, a kan bãkance da alwãshi, sunã ganin sa ibada ne.