Skip to content
الأنعَام /

Aya 71

6 : 71

Aya 71 of الأنعَام (6 : 71). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الأنعَام Ayoyi 165
6 : 71

قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."

Explanation & meanings · 1
  1. Shi kuma bã ya karɓãwa balle ya nufi wurin shiriyar da suke kiran sa ya tafi, sabõda yã riga yã fãɗi daga sama zuwa ƙasa, kuma ɗimuwa tã kãmã shi.