Skip to content
Aal'Imran /

Aya 159

3 : 159

Aya 159 of Aal'Imran (3 : 159). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Aal'Imran Ayoyi 200
Sura · Aal'Imran
Hausa · Gummi
3 : 159

فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ

Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.

Explanation & meanings · 1
  1. Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.