Skip to content
Jerin Surori /

الشعراء

الشعراء is chapter 26 of the Quran and has 227 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

227 Ayoyi Lambar Sura 26
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.

لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ

Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba!

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u.

إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةٗ فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ

Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ مُحۡدَثٍ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهُ مُعۡرِضِينَ

Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.