Skip to content
الشعراء /

Aya 189

26 : 189

Aya 189 of الشعراء (26 : 189). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الشعراء Ayoyi 227
26 : 189

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ

Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.

Explanation & meanings · 1
  1. An ruwaito cewa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi-sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nema daga Shu'aibu da a jefa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya.