Skip to content
Jerin Surori /

الفُرقَان

الفُرقَان is chapter 25 of the Quran and has 77 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

77 Ayoyi Lambar Sura 25
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

تَبَارَكَ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡفُرۡقَانَ عَلَىٰ عَبۡدِهِۦ لِيَكُونَ لِلۡعَٰلَمِينَ نَذِيرًا

Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta.

ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖ فَقَدَّرَهُۥ تَقۡدِيرٗا

wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa.

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗ لَّا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ وَلَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا وَلَا يَمۡلِكُونَ مَوۡتٗا وَلَا حَيَوٰةٗ وَلَا نُشُورٗا

Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa.

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٌ ٱفۡتَرَىٰهُ وَأَعَانَهُۥ عَلَيۡهِ قَوۡمٌ ءَاخَرُونَۖ فَقَدۡ جَآءُو ظُلۡمٗا وَزُورٗا

Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana.

وَقَالُوٓاْ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٱكۡتَتَبَهَا فَهِيَ تُمۡلَىٰ عَلَيۡهِ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا

Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma."