الرميصاء أو الغميصاء بنت ملحان الأنصارية
الإسم
Rumaisa’u ko kuma Ghumaisa’u diyar Milhan mutumiyar Madina
اسم الشهرة
Ummu Sulaim Allah ya yarda da ita
نبذة مختصرة
Ummu Sulaim diyar Milhan dan Khalid dan Zaid mutuniyar Madina, babar Anas ‘yar uwar Ummu Haram, sahabiya ce mai girma, tana da riwaya, lakabinta Ghumaisa’u, ana cewa kuma: Rumaisa’u, sunanta Sahlatu, ana cewa kuma Ramlatu, ana kuma cewa Rumaisa, ana cewa: Unaikatu, ana cewa kuma: Mulaikatu, ya tabbata daga Anas daga annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: Na shiga aljanna sai na ji motsi sai na ce wanene wannan? Sai suka ce: Ghumaisa’u diyar Milhan babar Anas dan Malik ce)). Annabi tsira da amincin Allah su Tabbata a gare shi, bai kasance yana shiga gida a Madina ba in banda gidan Ummu Sulaim saidai dakin iyalanshi , sai aka ce da shi (saboda me ?).( Ni ina lalla shin ta , an kashe dan’wanta yana tare da ni). Ta kasance tana auran Malik dan Nadar a lokacin Jahilyyah sai ta haifa masa Anas, a alokacin da Allah ya kawo mata Musulinci sai ta Musulunta tare da mutananta, ta kuma bijirowa mujinta da Musulunci sai ya yi fushi da ita ya gudu zuwa Sham ya mutu, ta rasu shekara ta 30, bayan hijira.