Skip to content

الزبير بن العوام بن خويلد الأسدي

الإسم

Zubairu dan Awwam da Khuwailid Daga Asad.

اسم الشهرة

Al-zubair Bin Al-Awwam -Allah yarda da shi-

نبذة مختصرة

Zubairu dan Awwam dan Khuwailid dan Asad dan abdil’uzzah dan Kusayy dan Kilab bakuraishe ne Daga Asad, baban Abdullah, sahabi ne mai girma, shi ne baharawen Manzan Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma dan gwaggwansa, daya daga cikin mutane goman da aka yi musu shaida da aljanna, kuma daya cikin mutane shida na Shurah, baffan Zubairu ya kasance yana daure shi a tabarma ya hura masa hayaki domin ya mayar da shi kafirci, sai ya ce: Ba zan kafirce ba har abada. Daga Urwah ya ce: Sara uku na takobi sun kasance a jikin Zubair na kasance ina sanya yatsuna a cikinsu, biyu a ranar Badar, dayan kuma a ranar Yarmuk, an kashe shi a shekara ta 36, bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
الجرح والتعديل لابن أبي حاتم (3/ 578) رجال صحيح مسلم (1/ 211) الاستيعاب في معرفة الأصحاب (2/ 510) الأعلام للزركلي (3/ 43) الإصابة في تمييز الصحابة (2/ 457-460).