Skip to content

خالد بن الوليد بن المغيرة المخزومي

الإسم

Khalid dan Walid dan Mughira Almakhzumi

اسم الشهرة

Khalid dan Walid Allah ya yarda da shi

نبذة مختصرة

Khalid dan Walid dan Mughira dan Abdullahi dan Makhzum bakuraishe Saifullahi, Abu Sulaiman sahabi ne mai daraja, ya kasance daya daga cikin manyan Kuraishawa a zamanin Jahilyyah, ya halarci yakoki tare da mushirikan Kuraishawa har zuwa lokacin Umurar Hudaibiya, sannan ya musulunta a shekara ta bakwai bayan Khaibar, an ce kuma kafin ita ne, ya halarci bude Makkah tare da Ma’aikin Allah- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ya kuma yi bajinta sosai, sannan ya halarci yakin Hunain da Da’if, kuma annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -ya aike shi domin rushe uzzah, ya kuma aikata. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce dangane da shi: “Madallah da bawan Allah dan dangi, Khalid dan Walid takobi daga takubban Allah, Allah ya zare shi a kan kafirai”. Ya rasu a 21 bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
الكنى والأسماء للإمام مسلم (1/ 370)، الجرح والتعديل لابن أبي حاتم (3/ 356)، مشاهير علماء الأمصار (ص: 56)، الإصابة (3/ 171 ط. هجر)، الأعلام للزركلي (2/ 300).