جندب بن جنادة بن سفيان بن عبيد الغفاري
الإسم
Jundubi dan Junadata dan Sufyan dan Ubaidu mutumin gifari
اسم الشهرة
Abu Thar Al'ghifari - Allah ya yarda da shi
نبذة مختصرة
Abu Zarr Alghifari, Jundubi dan Junadata, a mashahurin zance a sunan shi, sahabi ne mai daraja, ya musulunta da dadewa, an ce: shi ne na hudu a mutane hudu, wasu kuma suka ce: nabiyar din matane biyar, shi ne farkon wanda ya gaishe da annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi da gaisuwar Musulunci, ya je wurin annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shia Makkah sai ya ji maganganunsa, sai ya musulunta nan take, sai annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Ka koma wurin mutananka, ka basu bayanin (Musulunci) har al’amari na ya zo gareka, sai ya ce: Na rantse da wanda raina yake a hannun sa , sai yaya ta shi a tsaninsu , sai ya fita har sai da ya je Masallaci sai ya yi yekuwa ya daga muryarsa: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ina shaidawa annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzon da ne. Sai mutanan suka tashi suka dakke shi har suka yi masa rauni. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana farawa da Abu Zarr idan ya zo, yana neman labarinsa idan ba ya nan. Ya rasu a shekara ta 32 bayan hijira.