Skip to content

أويس بن عامر بن جزء بن مالك القرني

الإسم

Uwais ɗan Amir ɗan Juz’i ɗan Malik al-Ƙarni.

اسم الشهرة

Uwaisul Ƙarni

نبذة مختصرة

Baban Amru, Uwaisu Dan Amir Dan Ju’i Dan Malik alkarni, tabi’i ne Mai girma, yana cikin manyan tabi’ai, kuma daya daga masu yawan ibada na gaba, asalinsa daga Yaman ne, ya riski rayuwar Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Amma bai ganshi ba, sai ya zo wurin Umar Dan Khattab, sannan ya zauna a Kufa, ya tabbata cewa, shi ne fiyayyan Tabi’ai, kamar yadda ya tabbata daga Asir Dan Jabir, ya ce: Umar Dan Khattab ya kasance idan mayaka suka zo masa daga Yaman wadanda suke karfafar mayakan Musulunci a yaki sai ya tambaye su: Shin a cikinku akwai Uwaisu Dan Amir?,har ya zo ga Uwais Dan Amir, ya ce: Kai ne Uwaisu Dan Amir ? Ya ce: Eh,ya ce: daga murad daga Karn ? Ya ce Eh, ka kasance kama da kuturta Amma ta warke sai kamar fadin Dirham ? Ya ce: Eh, ya ce: kana da mahaifiya? Ya ce Eh, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: Uwais Dan Amir zai zo muku cikin dakarun Yaman,daga Murad, sannan daga Karn,ya kasance yana da kuturta Amma ya warke sai kamar shacin kwabo , yana da mahaifiya yana Mata biyayya, da zai rantse da Allah da Allah ya barrarantar (kubutar) da shi, idan ka sami iko ya roka maka gafarar Allah to ka yi)), sai ta je wurin Uwais ya ce: Ka roka mini gafarar (Allah), ya ce: Kai ne mafi kusa da tafiya nagartatta ka rokamin gafara, ya ce: Ka hadu da Umar ya ce Eh, sai ta roka masa gafara, sai mutane suka gane shi, sai ya wuce kawai. Asir ya ce Tufafinsa burda ce, duk lokacin da wani mutum ya gan shi sai ta ce: Ta ina Uwais ya sami wannan burdar, ya rasu shekara ta 37. Bayan hijira.

المراجع

Kari (1)
Sahih Muslim (4/ 1969، ح2542)، الطبقات الكبرى (6/204)، الطبقات لخليفة بن الخياط (ص: 246)، أسد الغابة (1/331)، سير أعلام النبلاء (4/519)، الأعلام للزركلي(2/ 32).