Skip to content

Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah

Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".

صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَانَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ»، وَعَنْ شِمَالِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ».

Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Hasan ne
Bayani

Annabin - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin ya juya daga sallarsa zai yi sallama a damansa da hagunsa shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren dama, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Halaccin sallama biyu a sallah, kuma ita tana daga rukunanta.

An so zuwa da ƙarin faɗin: (Da albarkarSa), a sashin lokuta; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana dawwama akanta ba.

Furta sallama biyu a cikin sallah rukuni ne na wajibi, amma yin waiwaye a tsakiyar furta su to (Mustahabbi ne) abin so ne.

Yana kamata ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah) a tsakiyar yin waiwaye ba kafinsa ko bayansa ba.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (2/ 239) (997).

Kari (5)

المجموع شرح المهذب (مع تكملة السبكي والمطيعي) النووي (3/ 479).

المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج.

النووي (4/ 153).

توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (2/ 291).