Skip to content

Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce

Daga Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce:

Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce.

يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ أُمَّ سَعْدٍ مَاتَتْ، فَأَيُّ الصَّدَقَةِ أَفْضَلُ؟، قَالَ: «الْمَاءُ»، قَالَ: فَحَفَرَ بِئْرًا، وَقَالَ: هَذِهِ لِأُمِّ سَعْدٍ.

Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
Hasan ne ta jimillar hanyoyinsa
Bayani

Mahaifiyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ta rasu, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafificin nau'ikan sadaka dan ya yi sadaka dashi ga mahaifiyarsa? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba shi labarin: Cewa mafificiyar sadaka ita ce ruwa, sai ya haƙa wata rijiya ya sanyata sadaka ga mahaifiyarsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin cewa ruwa yana daga mafificin nau'ikan sadaka.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunawa da Sa'ad zuwa ga sadakar ruwa; domin shi ya fi gamewar anfani a cikin al'amuran addini da duniya, kuma saboda tsananin zafi da buƙata da ƙarancin ruwa.

Nuni akan ladan sadaka yana zuwa ga mamata.

Biyayyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ga mahaifiyarsa - Allah Ya yarda da su -.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (3/ 109) (1681).

Sunanu Nasa'i (6/ 254) (3664).

Sunanu Ibn Majah (4/ 643) (3684).

Kari (1)

شرح سنن أبي داود للعباد (204/ 19).