Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

19 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Kaffarar bakance ita ce kaffarar rantsuwa».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce.
Hasan ne ta jimillar hanyoyinsa Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi