Skip to content
Jerin Surori /

البَلَد

البَلَد is chapter 90 of the Quran and has 20 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

20 Ayoyi Lambar Sura 90
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.

Explanation & meanings · 1
  1. Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu.

وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.

وَوَالِدٖ وَمَا وَلَدَ

Da mahaifi da abin da ya haifa.

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ

Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٞ

Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?