Skip to content
Jerin Surori /

الفَتح

الفَتح is chapter 48 of the Quran and has 29 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

29 Ayoyi Lambar Sura 48
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا

Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne.

لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imar Sa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya.

Explanation & meanings · 1
  1. Laifin Annabi wanda Allah Ya gãfarta, shĩ ne a lõkacin da ya fãra kiran mutãne zuwa ga bauta wa Allah, Shĩ kaɗai, mãsu bauta wa waɗansu abũbuwa sun ga laifinsa a wannan, sun yi ƙiyayya da shi sabõda haka, har suka yi yãƙi da shi, dõmin tsare ibãdarsu, da al'adunsu, har a lõkacin da Allah Ya bã shi rinjãye bayyananne a kansu, suka gãne amfãnin abin da yake kiran su zuwa gare shi na alheri, suka yãfe laifin da suke zato kuma suka so shi son da bã ya ƙãrewa har Tãshin Ƙiyãma. Wannan ni'imar Allah ce babba ga Annabinsa, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanya madaidaiciya, ita ce sharĩ'ar da Allah Ya bã shi, wadda ke jan jama'arsa a kan alheri har ya zuwa Tãshin ƙiyãma, kuma su tãshi a cikin alheri mafi girma, matuƙar dai sun bĩ ta, sun yi aiki da ita gwargwadon yadda ya nũna musu ita.

وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا

Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi.

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِيمَٰنٗا مَّعَ إِيمَٰنِهِمۡۗ وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima.

لِّيُدۡخِلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عِندَ ٱللَّهِ فَوۡزًا عَظِيمٗا

Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia.