Skip to content
Jerin Surori /

الصَّافَات

الصَّافَات is chapter 37 of the Quran and has 182 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

182 Ayoyi Lambar Sura 37
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفّٗا

Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا

Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.

Explanation & meanings · 1
  1. Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.

فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا

Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ

Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.