Skip to content
النَّحل /

Aya 125

16 : 125

Aya 125 of النَّحل (16 : 125). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النَّحل Ayoyi 128
16 : 125

ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Kira zuwa ga hanyar Ubangiji, Allah, yanã daga cikin abũbuwan kõyo daga Ibrãhĩm kuma kira zuwa ga Allah na daga cikin ni'imõmin Allah ga mai kiran da wanda ake kiran sa'an nan zaman kiran da hikima da wa'azi mai kyau, ni'ima ce ga mai yi da waɗanda ake kira zuwa ga shiriyar duka. Abin da ake cħwa Hikima shĩ ne a yi magana a kan hujja wadda abõkin husũma bã zai iya kauce mata ba.