Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
"Wanda ya ce: Da suna Allah wanda wani abu ba ya cutuwa tare da sunanSa a cikin ƙasa, ko cikin sama, Shi ne Mai yawan ji Masani”. sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai ya wayi gari, wanda ya faɗeta lokacin da ya wayi gari sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai shiga maraice", ya ce: Sai shanyewar ɓarin jiki ya samu Aban ɗan Usman, sai mutumin da ya ji hadisin daga gare shi ya fara kallonsa, sai ya ce masa: Me yasa meka kake kallona? Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, sai dai ranar da abinda ya sameni ya sameni a cikinta na yi fushi sai na manta ban fadi addu'ar.
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma Ahmad
"Shugaban Istighfari shi ne ka ce: Ya Allah Kai ne Ubanjina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai ka halicceni, kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan alkawarinKa gwargwadon ikona, ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, ina ikirari gareKa da ni'amarKa gareni, kuma ina ikirari da zunubina, to Ka gafarta mini domin cewa babu mai gafartawa sai Kai". ya ce: "wanda ya fadeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a wannan rana kafin ya yi yammaci to yana cikin 'yan aljanna, wanda ya fadeta da daddare yana mai sakankancewa da ita sai ya mutu kafin ya wayi gari to yana cikin 'yan aljanna".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fita daga wurinta da sassafe yayin da ya yi sallar Asuba, alhali tana wurin sallarta, sannan ya dawo bayan hantsi ya daga, alhali tana nan a zaune, sai ya ce: «Ba ki gusheba a kan halin da na barki a kansa?» Ta ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa, adadin halittar Sa, da yardar kanSa, da nauyin Al’Arshin Sa, da tawadar kalmomin Sa).
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi