Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne".
«مَلْعُون مَنْ أتَى امرأتَه في دُبُرِها».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga miji ya zo wa matarsa ta duburarta; cewa shi tsinanne ne abin korewa daga rahamar Allah, kuma shi babban laifi ne cikin manyan laifuka.
Haramcin zakkewa mata ta duburarsu.
Jin daɗi daga mata a koma bayan duburarta na jikinta ya halatta.
Musulmi yana zakkewa mace ne ta farjinta kamar yadda Allah Ya umarce shi; amma ta dubura to a cikin hakan akwai ɓata ɗabi'a, da tozarta zuriya, da saɓawa abinda nagartattun ɗabi'u suke a kansa, da kuma cutuka masu kaiwa ga ma'auratan.
Sunan Abi Dawud (3/ 489) (2162).
Sunanul Kubura Na Nasa'i (8/ 200) (8966).
Musnad Ahmad (15/ 457) (9733).
Kari (8)
نيل الأوطار.
للشوكاني (6/ 237).
سبل السلام.
للصنعاني (2/ 202).
توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام.
للبسام (5/ 346).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (4/ 535).