Skip to content

Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki

Daga Imaran Ɗan Husain Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na kasance Ina da basir, sai na tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da sallah sai ya ce:

Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki.

«صَلِّ قَائِمًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ».

Bukhari ne ya rawaito shi.
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana asali a Sallah shi ne a yi ta a tsaye, sai idan ba za a iya ba, sai a yi ta a zaune, idan ba zai iya sallar a zaune ba, to, ya samu ya yi a gefen jikinsa.

Ma"anonin Kalmomi

بواسير: جمع باسور، وهو ورم يصيب مقعدة الإنسان.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Sallah ba ta faɗuwa muddin hankali na nan, sai ya kasance daga wannan yanayin, zuwa wancan yanayin gwargwadon damar da yake da ita.

Sauƙi da rangwamen Musulunci cewa bawa zai aikata ibada yadda yake da iko.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (2/ 48) (1117).

Kari (4)

توضيح الأحكام من بلوغ المرام.

لعبدالله البسام (2/ 322).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (3/ 202).