Skip to content
النِّسَاء /

Aya 101

4 : 101

Aya 101 of النِّسَاء (4 : 101). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 101

وَإِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَقۡصُرُواْ مِنَ ٱلصَّلَوٰةِ إِنۡ خِفۡتُمۡ أَن يَفۡتِنَكُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْۚ إِنَّ ٱلۡكَٰفِرِينَ كَانُواْ لَكُمۡ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.

Explanation & meanings · 1
  1. Rage salla a nan ba ana nufin sallar kasaru ta tafiya ba, wanda take ta tabbata da sunna. Wannan rage salla, shi ne sallar tsõro wadda ake yi gwargwadon hãlin da ake ciki na tsõro. Idan yana yiwuwa a yi ta da lĩmãmi, sai ya kasa jama'a kashi biyu, to, sai a yi kamar yadda ãya ta tafe zã ta yi bayãni, idan kuwa bã zai yiwu ba, sai a yi yadda hãli ya sauƙaƙa duka, kamar a ãyã ta 239 daga Suratul Baƙara.