25 : 60
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱسۡجُدُواْۤ لِلرَّحۡمَٰنِ قَالُواْ وَمَا ٱلرَّحۡمَٰنُ أَنَسۡجُدُ لِمَا تَأۡمُرُنَا وَزَادَهُمۡ نُفُورٗا۩
Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra musu gudu.
Explanation & meanings · 1
- Kõ sun san gaskiyar abin daaka kira su zuwa gare shi, bã zã su yi ɗã'ã ba, dõmin wai sunã jin nauyi su karɓi umurni daga wani mutum.