النعمان بن ثابت الكوفي الإمام
الإسم
Nu’umanu dan Sabitu mutumin Kufa, Imam
اسم الشهرة
Abu Hanifah
نبذة مختصرة
Abu Hanifa, Nu’uman dan Sabit dan Zodi mutumin Kufa, Imam malamin addini, ya kasance mai tsantseni mai tsoron Allah, yana da tsananin kin ya ga ana aikata abinda Allah ya haramta, an bijiro mishi da duniya da dukiya mai yawan gaske, sai ya yi watsi da ita can bayansa, har ta kai ga yi masa bulala, domin ya karbi alkalanci, ko baitul mali ya kuma ki karba. Zahabi ya ce: ((Ya kamata tarihinsa a ware shi daban ne a mujalladi biyu, Allah ya yarda da shi). Imam Ahmada ya ce dangane da shi: ( Lalle Abu Hanifa dangane da ilimi da tsantseni da zuhudu da fifita lahira to yana da matsayi na musamman babu wanda yake riskarsa, hakika an yi mishi bulala domin ya bi Mansur bai yi ba), Allah ya yi masa rahama ya kuma yarda da shi. Imam Shafi’i ya ce: An tambayi Malik dan Anas: Shin ka ga Abu Hanifa kuma ka tattauna da shi ? Sai ya ce: Eh, na ga mutum da zai ga wannan dirkar ta dutse ce ya ce ta zinariya ce da ya tabbatar da hujja akan hakan)). Ya rasu shekara ta 150, bayan hijira.