أم حكيم بنت الحارث بن هشام
الإسم
Ummu Hakim diyar Haris dan Hisham
اسم الشهرة
Ummu Hakim diyar Haris dan Hisham, Allah ya yarda da ita
نبذة مختصرة
Ummu Hakim diyar Haris dan Hisham dan Mughira daga Banu Makhzum, sahabiya ce mai girma, ta halarci yakin Uhudu tare da mushirikai, sannan ta musulunta ranar fathu Makkah, mujinta Ikrimatu dan Abu Jahal ya kasance ya gudu zuwa Yaman, sai ta bi shi da izinin annabi tsira da amincin Allah su Tabb a gare shi, sai ta zo da shi ya kuma musulunta, sannan ta fita tare da shi domin yakar Rumawa , sai ya yi shahada, sai Khalid dan Sa’ad dan As ya aure ta dab da yakin Marjul Sifir kudu da Dimashk (Damascus) lokacin da ya yi shahada a yakin, sai Ummu Hakim ta yi damara da tufafinta ta tamke tana alamar turare (na amarci), suka gwabza yaki a bakin kogin nan, daidai gadar da a yanzu ake cikaranta da gadar Ummu Hakim, an kasheta a daidai mahadar Fustas, a inda Khalid ya tare da ita bakwai cikin Rumawa, an kasheta shekara ta 14, bayan hijira.